Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta yi bayyana mafi kyawu a gasar wasannin motsa jiki ta duniya

Tawagar Najeriya ta yi bayyana mafi kyawu a gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da ke gudana a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Wasu 'yan wasan Najeriya da ke wakiltar kasar a gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da kasar Kenya ke karbar bakunci.
Wasu 'yan wasan Najeriya da ke wakiltar kasar a gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da kasar Kenya ke karbar bakunci. © Africa Top Sports
Talla

Kawo yanzu tawagar Najeriyar ta lashe lambobin yabon Zinare 4 da Tagulla 3.

Wannan nasara ta kai kasar zuwa matsayi na 3 a gasar wasannin motsa jikin ta duniya biye da Finland mai Zinare 4 da Azurfa 1, yayin da mai masaukin baki Kenya ke matsayi na 1 bayan lashe Zinare 8, Azurfa 1 da kuma Tagulla 7.

A halin da ake ciki, Ministan Wasannin Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa kyaututtukan kudi na jiran 'yan wasan kasar da suka ci lambobin yabo a gasar da ke gudana.

A cewar Ministan, wanda ya lashe lambar yabo ta Zinare zai dafe kyautar tsabar kudi dala dubu 5000, sai ladan dala dubu 3000 ga wadanda suka lashe Azurfa, yayin da dala dubu 2 ke jiran ‘yan wasan da suka lashe  lambobin Tagulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.