Isa ga babban shafi
Wasanni - Olympics

Kamfanin PUMA ya soke yarjejeniyar shekaru 4 da ya kulla da Najeriya

Fitaccen kamfanin da ke sana’anta kayan wasanni na kasar Jamus PUMA ya soke yarjejeniyar shekaru hudu da ya kulla tsakaninsa da hukumar kula da wasannin motsa jiki ta Najeriya.

Katako dauke da tambarin kamfanin Puma a cibiyar siyayya da ke kauyen Belaya Dacha da ke wajen Moscow, babban birnin kasar Rasha.
Katako dauke da tambarin kamfanin Puma a cibiyar siyayya da ke kauyen Belaya Dacha da ke wajen Moscow, babban birnin kasar Rasha. © REUTERS/Grigory Duko
Talla

Puma ya sanar da matakin ne cikin wasikar da ya mikawa Najeriyar a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa ya yanke shawarar soke yarjejeniyar ce sakamakon abubuwan da suka wakana a gasar Olympics da ke gudana a Japan, ba tare da yayi karin bayani ba.

Sai dai ana kyautata zaton cewa, raba garin da PUMA yayi da Najeriya na da alaka da rikicin jagoranci tsakanin hukumar kwamitin kula da wasannin motsa jikin kasar da Ibrahim Gusau ke jagoranta da kuma Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare.

A baya bayan nan wata majiya ta ruwaito ministan wasannin Najeriya Sunday Dare na shan alwashin  haramtawa 'yan wasan Najeriya sanya kayan PUMA a gasar Olympics da suke halarta.

A shekarar da ta gabata ne kuma hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta wanke shugaban kwamitin wasannin motsa jikin Najeriya Ibrahim Gusau da mataimakinsa Sunday Adeleye bisa zargin cin hanci da rashawa da ma'aikatar wasanni ke musu masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.