Matashin ɗan Najeriya ya zama lamba ɗaya a duniyar kwallon Tebur
Wani matashin dan Najeriya ya zama lamba daya a wasan kwallon teburi ajin maza na ‘yan kasa da shekaru 11 a duniya.
Wallafawa ranar:
Matashin dan wasan Musa Mustapha wanda ke zaune a Abuja yana daga cikin ‘yan wasan kwallon tebur na Najeriya da suka lashe Gasar Wasannin Matasa ta ITTF a shekarar 2019 a kasar Ghana.
Shekaru uku kenan da suka gabata Hukumar kwallon tebur ta duniya ke bibiyar dan wasan, tun bayan da ya fara buga gasar cin kofin kwallon tebur ta Najeriya a birnin Lagos.
Kafin Mustapha wata 'yar masar ke rike da ajin mata
Mustapha ya zama ɗan Afirka na biyu da aka zaba a matsayin lambobi na ɗaya a duniya, baya ga Hana Goda ‘yar kasar Masar da itama ta kasance ta farko a ajin mata ‘yan kasa da shekaru 15 a shekarar 2020.
A cikin jerin ‘yan wasan da hukumar kwallon Tebur din da fitar Mustapha yazo na daya a duniya da maki 128, a ‘Yan kasa da shekaru 11, yayin da ya kasance na 17 a cikin rukunin ‘yan kasa da shekaru 13.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu