Isa ga babban shafi
Senegal - wasanni

Macky Sall ya soke ziyara zuwa waje saboda tarbar 'yan wasan Senegal

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin murnar nasarar da kungiyar kwallon kafar kasar ta samu a gasar cin kofin nahiyar Afirka na farko bayan nasarar da suka yi kan Masar da ci 4 – 2 a bugun finareti, bayan kwashe shekaru 60 suna jira.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, yayin jawabi 11,2020.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, yayin jawabi 11,2020. © AFP / Lionel Mandeix
Talla

Sall, wanda ya kamata ya ziyarci Comoros a karshen balaguron da ya yi a Masar da Habasha, ya soke tafiyar don tarbar ‘yan tawagar  Teranga a birnin Dakar a wannan Litinin.

Dan wasan Liverpool Sadio Mane ne ke jagorantar tawagar Senegal ta doke Masar na Mohamed Salah da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan tashi wasan babu ci duk  da karin lokaci.

Bayan barar da damar har sau biyu a wasannin karshe da Senegal ta kai 2002 da 2019, a karshe Senegal ta dauki kofin gasar cin kofin Afirka na farko.

Tashar talabijin ta kasar Senegal ta ruwaito cewa shugaba Sall zai mikawa ‘yan wasan lambar yabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.