Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Aubameyang ya fice daga gasar AFCON a Kamaru

An sahale wa dan wasan gaba na Arsenal Pierre Emerick Aubameyang da ya fice daga tawagar Gabon da ke fafatawa a gasar cin kofin Afrika a Kamaru sakamakon fama da cutar Korona.

Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon na fama da cutar Korona
Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon na fama da cutar Korona GABRIEL BOUYS AFP/File
Talla

Yanzu haka Aubameyang zai koma London domin ci gaba da samun kulawa karkashin kungiyarsa ta Arsenal kamar yadda kocin tawagar Gabon ya bayyana a yau Litinin.

Kazalika Gabon ta mayar da dan wasanta na tsakiya Mario Lemina zuwa kungiyarsa ta Nice da ke Faransa, bayan dan wasa ya gaza buga ko da minti guda a wasanni guda biyu da kasarsa ta yi da Comoros da Ghana a gasar ta cin  kofin Afrika.

Shi ma dai Lemina na fama ne  da cutar Korona,  abin da ya hana shi haskawa a gasar ta Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.