Isa ga babban shafi
Kwallon Kwando

Najeriya ta sake bada mamaki a wasan kwallon kwando

Tawagar kwallon kwandon Najeriya ta D’Tigers na ci gaba da nuna bajinta a wasannin sada zumuncin da take yi domin kara kintsawa gasar Olympics da ake shirin farawa nan da ‘yan kwanaki a birnin Tokyo na kasar Japan.

'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya na D'Tigers yayin fafatawa da Argentina a wasan sada zumunci.
'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya na D'Tigers yayin fafatawa da Argentina a wasan sada zumunci. © news.ncbn.ng
Talla

A ranar Litinin tawagar kwallon kwandon Najeriyar ta D’Tigers ta samu lallasa takwararta ta Argentina da kwallaye 94-71 yayin fafatawar da suka yi a birnin Las Vegas na kasar Amurka.

Argentina da Najeriyar ta doke a jiya dai ita ce ta hudu wajen kwarewa a wasan kwallon kwando a duniya.

A ranar Lahadin da ta gabata Najeriya ta kafa tarihin zama kasa ta farko daga nahiyar Afrika da ta samu nasara kan Amurka a wasan kwallon Kwando, bayan da doke ta da kwallaye 90-87.

Karo na biyu kenan da aka kara tsakanin Najeriya da Amurka, bayan fafatawar da suka yi shekaru 9 da suka gabata, lokacin da Amurkan ta lallasa Najeriya da kwallaye 156-73 a gasar Olympics da a waccan lokacin birnin London ya karbi bakuncinta.

A ranar 25 ga watan Yuli, Najeriya za ta fafata wasanta na farko da Australia a gasar Olympics ta bana cikin rukuni na biyu da ya kunshi Italiya da Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.