Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool za ta hana 'yan wasanta damar taka leda a gasar Olympic

Da yiwuwar babu ko da dan wasan Liverpool daya da zai halarci wasannin Olympic da zai gudana a birnin Tokyo na Japan, wasannin gasar da za su kankama a watan gobe bayanda annobar covid-19 ta tilasta dage gasar daga bara da aka tsara zuwa bana.

Wasu daga cikin 'yan wasan Liverpool.
Wasu daga cikin 'yan wasan Liverpool. GABRIEL BOUYS AFP
Talla

Sakon da kungiyar ta Liverpool ta aikewa kasashen da ‘yan wasansu ke taka mata leda, ta ce bata fatan bai wa kowanne dan wasa damar takawa kasarsa leda a wasannin na Olympic ciki har da Mohammed Salah na Masar wanda kasar sa ke maitar ganin ya taka mata leda a wasannin.

Za dai a faro wasannin na Olympics da corona ta hana bara ne a ranar 22 ga watan yuli mai kamawa a kuma karkare a ranar 7 ga watan Agusta.

Duk da sakon na Liverpool shugaban hukumar kwallon kafar Masar Ahmed Mujahed ya bayyana fatan dan wasan ya iya samun alfarmar takawa kasar Leda.

Salah mai shekaru 29 fiye da shekara guda kenan anan dambarwa kan yiwuwar ya rasa damar takawa kasar tasa leda a wasannin na Olympic.

A cewar Mujahed ba ya tilastawa Salah ya takawa Masar leda a wasannin gasar amma abu ne mai matukar wahala ga kasar da shi kansa dan wasan, a iya zuwa gasar ba tare da shi ba.

Baya ga Salah ‘yan wasa irinsu Minamino da Ibrahim Konate dukkaninsu bazasu samu damar dokawa kasashensu wasannin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.