Isa ga babban shafi
Wasanni

Kasashen Afrika za su tafi Turai don fafata wasannin sada zumunci

Shirye shirye sun yi nisa tsakanin kasashen Afrika, wadanda tawagoginsu na kwallon kafa za su koma filaye don fafata wasanin da suka shafe akalla watanni 10 ba tare da bugawa ba, saboda annobar coronavirus.

Wasu 'yan kwallon kafar nahiyar Afrika
Wasu 'yan kwallon kafar nahiyar Afrika Reuters
Talla

A wannan karon mafi akasarin tawagogin kwallon kafar kasashen na Afrika za su yi tattaki ne zuwa kasashen Turai domin fafatawa wasannin sada zumunci a can, tsakanin 5 zuwa 13 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumar FIFA ta bada dama.

Babban dalilin kasashen Afrikan na yin balaguro zuwa Turan kuwa shi ne kasancewar mafi akasarin ‘yan wasansu na kungiyoyin dake nahiyar ne, abinda zai saukaka musu aikin hada kan ‘yan wasan nasu.

Bayanai dai sun ce kamaru za su yi tattaki ne zuwa kasar Netherlands, Guinea za ta je Portugal, yayinda Najeriya, Ivory Coast da Tunisia za su yi tattaki zuwa kasar Austria, inda a nan ne za su fafata dukkanin wasannin sada zumuncin da za su yi a tsakaninsu.

A Netherlands Kamaru za ta fafata da Japan, yayinda kuma Guinea za ta kara da Cape Verde, da kuma Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.