Isa ga babban shafi
Kyautar Marc Vivien Foe

Jean Michael Seri ne ya lashe kyautar Marc Vivien Foe

Jean Michael Seri dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Nice dake kasar Faransa ne aka zaba a matsayin dan wasan da ya cancaci lashe kyautar da aka baiwa sunan dan kwallon kasar Kamaru da ya rasu a fagen wasa ranar 26 ga watan Yuni shekara ta 2003 a filin wasa na Gerland dake Lyon.

Jean Michaël Seri dan wasan da ya lashe kyautar Marc Vivien Foe na shekarar 2017
Jean Michaël Seri dan wasan da ya lashe kyautar Marc Vivien Foe na shekarar 2017 AFP/Valéry Hache
Talla

Gidan rediyon Faransa RFI, da kaffar Talabijin na France 24 ne suka shirya wannan kyauta tare da bai wa kwarraru damar tanttance daya daga cikin 'yan wasa goma da suka hada da Jean Michael Seri na kasar Cote D’Ivoire mai taka leda a Nice da ya samu maki 255, Ryad Boudebouz na kungiyar Montpelleir dan kasar Aljeriya da ya samu maki 126.

Benjamin Moukanjo dake taka leda a Lorient dan kasar Kamaru ya samu maki 97, yayinda Younes Belhanda dan kasar Moroko mai buga wasa a Nice ya samu maki 42, Steve Mounie dan kasar Benin mai buga wasa a Montpellier da maki 24, sai kuma Cheikh Ndoye daga kulob na Angers kuma dan kasar Senegal da ya samu maki 17.

Sauran hada da Francois Kamano daga Bordeaux kuma dan kasar Guinee, mai maki 10, Stevve Yago dan Burkina Faso mai taka leda a Toulouse ya samu maki 4 sai Serge Aurier dake haskawa a PSG dan Cote d’ivoire da maki 1.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.