Dubban matan Iran sun nuna maitarsu kan kwallon kafa
Dubban ‘yan matan Iran sun yi tururuwar saye tikitin kallon wasan da kasar za ta yi da Cambodia a birnin Tehran a gobe Alhamis a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayan hukumomin Iran sun tabbatar wa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA cewa, a wannan karo za su amince wa mata shiga fili domin kallon wasa kai tsaye, yayin da aka ware bangaren da mata zalla za su zauna a filin na Tehran.
Hukumomin Iran sun ce, cikin ‘yan mintoci kalilan, matan suka saye daukacin tikiti dubu 3 da 500 da aka ware musu a shafin intanet.
Kimanin shekaru 40 kenn da Iran ta haramta wa mata shiga filin wasa kwallon kafa bisa dalilai na addinin Islama.
Sai dai a watan jiya Hukumar FIFA ta umarci Iran da ta bude kofa ga matan domin shiga filayen wasanni biyo bayan mutuwar wata matashiya da aka cafke ta a lokacin da take kokarin shiga fili bayan ta yi shigar maza.
Matshiyar da ake yi wa lakabi da Blue Girl ta cinna wa kanta wuta har lahira saboda fargabar fuskantar hukuncin dauri a gidan yari
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu