Isa ga babban shafi
wasanni

Manchester United ta biya Mourinho kudin sallama

Manchester United ta biya tsohon kocinta Jose Mourinho da tawagar ma’aikatansa Pam miliyan 19.6 a matsayin kudin sallama bayan ta raba gari da shi a cikin watan Disamban da ya gabata.

Jose Mourinho
Jose Mourinho REUTERS/Pedro Nunes
Talla

Manchester United ta bayyana adadin kudin ne bayan ta fitar da wani sakamakon alkaluman kudaden da ta kashe a bara.

Kungiyar ta salami Mourinho ne sakamakon rashin tabuka abin kirki a kakar bana, abin da ya jefa su mataki na 11 a teburin gasar bayan lallasar da suka sha a hannun Liverpool da ci 3-1.

Tuni magajinsa da aka nada a matsayin kocin rikon kwarya, Ole Gunnar Solskjaer ya lashe wasanni 10 daga cikin 11 da ya jagoranci kungiyar kafin a ranar Talatar da ta gabata, ya sha kashi a hannun PSG a gasar zakarun nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.