Isa ga babban shafi
Wasanni

Za mu iya lashe kofin zakarun Turai na bana - Courtois

Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois ya ce kungiyarsa za ta yi samun nasarar lashe kofin gasar zakarun Turai na bana, kuma karo na 4 a jere.

Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois.
Mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois. Reuters
Talla

Courtois ya bayyana kwarin gwiwar tasa, yayin ganawa da manema labarai, gabanin wasan da za su fafata yau Laraba tsakaninsu da Ajax a birnin Amsterdam.

A baya bayan na dai Real Madrid ta samu farfadowa daga durkushewar da ta yi a gasar La Liga, inda ta rage yawan tazarar makin da Barcelona ta ba ta, bayan samun nasarar lallasa Atletico Madrid da kwallaye 3-1 a makon da ya kare.

Zalika a gasar cin kofin Copa del Rey na Spain Real Madrid ta kai zagayen kusa dana karshe, wanda a wasan zagayen na farko, aka tashi wasan tsakaninta da Barcelona 1-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.