Isa ga babban shafi
Wasanni

Monaco ta nada Henry Thierry sabon manaja

Kungoyar Kwallon kafar Monaco da ke France ta nada tsohon tauraron kungiyar Arsenal da Barcelona, Thierry Henry a matsayin mai horar da ‘Yan wasa domin maye gurbin Leonardo Jardem da ta kora saboda kungiyar ta kasa kokari a karkashin sa a cikin wannan kakar wasanni.

Dan wasan kwallon kafa, Thierry Henry
Dan wasan kwallon kafa, Thierry Henry REUTERS/Sergio Perez/File Photo
Talla

Wannan shine karo na farko da Henry zai rike babbar kungiya a matsayin mai horar da ‘Yan wasa, tun bayan yayi ritaya daga buga kwallo.

 

Kafin wannan nadin, tsohon tauraron dan wasan da ya lashe kofin Turai da na duniya da kasar Faransa, yana aiki ne a matsayin mataimakin mai horar da kungiyar kasar Belguim a karkashin Roberto Martinez tun shekarar 2016, wanda ya taimaka musu zuwa matsayi na uku a gasar cin kofin duniyar bana.

 

Henry mai shekaru 41 ya sanya hannu kan kwangilar da zata kai shi watan Yunin shekarar 2021 a kungiyar da ya fara wasan sa a matsayin kwararen dan kwallo.

 

Henry na daga cikin yan wasan da suka samu horo tun suna kanana a kungiyar Monaco, yayin da ya fara buga mata wasa a shekarar 1994, inda a shekarar 1997 zuwa 1998 ya jefa kwallaye 7 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, a karkashin jagorancin Arsene Wenger, nasarar da ta kaisu wasan kusa da na karshe da suka sha kaye a hannun Juventus.

 

Bayan ya kwashe shekaru 5 a Monaco, Henry ya koma kungiyar Juventus da Arsenal da Barcelona kafin karkarewa da New York Red Bulls.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.