Isa ga babban shafi
wasanni

Ba zan sake buga kwallo a kungiyar Turai ba- Messi

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya ce, yana ci gaba da amanna cewa, ba zai taba buga wa wata kungiyar kwallon kafa a nahiyar turai tamaula ba.

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallaye sama da 500
Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallaye sama da 500 REUTERS/Juan Medina
Talla

Dan wasan ya shafe rayuwarsa ta ajin manya a duniyar tamaula yana taka leda a Barcelona, in da ya ci ma ta kwallaye 552, yayin da a baya aka yi ta rade-radin cewa zai koma Manchester City .

Dan wasan mai shekaru 30 ya ce, akwai yiwuwar ya koma kasarsa ta asali wato Argentina don buga kwallo a kungiyar Newell’s Old Boys, amma lallai ba zai sake buga wa wata kungiya a Turai ba baya ga Barcelona.

Messi ya ce, Barcelona ce kawai za ta ci gaba da kasancewa kungiyarsa a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.