Isa ga babban shafi
wasanni

Wani lauyan Masar ya shigar da karar Real Madrid kan Salah

Wani lauya mai zaman kansa a Masar ya shigar da karar Real Madrid tare da neman diyyar dala biliyan guda daga hannun kaftin dinta Sergio Ramos sakamakon abin da ya kira ganganci da kuma karfi daya nuna kan dan wasan Masar da ke taka leda a Liverpool Mohamed Salah yayin wasan karshe na lashe kofin zakarun turai wanda Real din ta lallasa Liverpool da ci 3-1.

A cewar lauyan Bassem Wahba da gangan ne Ramos ya yi sanadin raunin na Salah.
A cewar lauyan Bassem Wahba da gangan ne Ramos ya yi sanadin raunin na Salah. REUTERS/Phil Noble
Talla

Lauyan Bassem Wahba, ya ce da gangan ne Ramos din ya tankwara hannun Salah tare da hankade inda a fada kan hannunsa na hagu dalilin kenan da ya haddasa masa karaya a kashin a kafadarsa.

Mr Wahba ya kuma bukaci hukumomin kwallon kafa na FIFA da UEFA su tabbatar da ganin an hukunta Ramos tare da biyan adadin diyyar ta Dala biliyan 1 kan abin da yayiwa Mohamed Salah dan wasan da Masar din ke fatan zai kai ta ga nasara a gasar cin kofin duniya ta bana a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.