Ana bincike kan barazanar kashe golan Liverpool
Rundunar ‘yan sandan Merseyside ta ce, tana da masaniya game da barazanar kisan da aka yi wa mai tsaren ragar Liverpool, Loris Karius bayan kammala wasan karshe tsakaninsu da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai.
Wallafawa ranar:
An yi wa golan barazanar hallaka shi da iyalansa saboda kura-kuran da ya yi har aka zura musu kwallaye 2 a wasan wanda Madrid ta samu nasara da kwallaye 3-1.
Rundunar ‘yan sandan ta ce, tana gudanar da bincike game da barazanar wadda aka yi ta shafukan sada zumunta.
Karius mai shekaru 24 kuma dan asalin kasar Jamus, ya bai wa magoya bayan Liverpool da sauran ‘yan kungiyarsa hakuri kan kura-kuransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu