Isa ga babban shafi

Ronaldinho zai angwance da 'yan mata 2

Tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Ronaldinho na shirye-shiryen aurar mata biyu lokaci guda, a watan Agusta mai zuwa.

Ronaldinho tare da amarensa.
Ronaldinho tare da amarensa. Twitter
Talla

‘Yan matan na Ronaldinho sun hada da Priscilla Coelho da Beatriz Souza.

Amaren na Ronaldinho sun dauki lokaci suna zaune lafiya, babu tashin hankali tare da tsohon tauraron kwallon kafar tun a watan Disambar bara, a katafaren gidansa na euro miliyan 5 da ke birnin Rio de Janeiro.

A shekarar 2016 Ronaldinho ya hadu da Beatriz amma ya ci gaba da soyayyarsa da Priscilla da suka kwashe shekaru tare.

An rawaito cewa dukkanin Amaren goben na karbar alawus na euro 1,500 a duk wata daga ango Ronaldinho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.