Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldinho ya miƙa godiyarsa ga tamaula

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil wanda yanzu haka ya yi murabus, ya miƙa sakon godiyarsa ga wata ƙwallo da kuma duk waɗanda suka taimaka masa a tsawon lokacin da ya kwashe yana wasa.

Dan wasan kwallon kafa na Brazil Ronaldinho Gaúcho.
Dan wasan kwallon kafa na Brazil Ronaldinho Gaúcho. Ronald Martinez/Getty Images/AFP
Talla

A ta bakin Ronaldinho, ya ce ‘Bayan na kwashe shekaru 30 ina taka leda, zan ajiye wannan abu da na ci ma buri tun ina ƙarami na…Burin da na cimma a rayuwata.

Ina gode miki ball, wadda kika zama mai ƙarfafa min guiwa a tsawon wannan lokaci, kuma kika kasance tare da ni a lokutan samun nasara.”

Ya ƙara da cewa ‘Mutane sun san ni a matsayin mutum mai kunya, ni ba mutum ne mai tsawaita kalami ba a lokacin da nake magana, to amma tun daga cikin kokon raina ina gode wa duk waɗanda suka taimaka min na yi abinda na fi ƙauna a rayuwata.’

Ronaldinho dai ya lashe ƙyaututtuka da dama a tsawon lokacin da ya kwashe yana buga kwallo, tun daga kungiyar Gremo da ke Brazil, zuwa Paris Saint-Germaine da ke Faransa, da Barcelona a Spain, da A.C Milan da ke Italiya, kafin ya sake komawa ƙasarsa Brazil.

Ya lashe kofin nahiyar Amurka a 1999, da kofin duniya a 2002, da kofin zakarun kungiyoyin Turai a 2006, da Copa Libertadores a 2013, kuma ya samu kyautar Ballon d’Or a 2005.

Ya ɗdaga kofin La liga na Spaniya sau 2, ya ɗaga kofin Seria A na Italiya sau 1, sannan ya ɗaga kofin FIFA Confederation Cup.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.