Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyar PSG ta lallasa Dijon da kwallaye 8-0

Dan wasa mafi tsada na duniya Neymar Jr ya zura kwalaye 4, a wasan gasar Ligue 1 na kasar Faransa da kungiyarsa ta PSG ta lallasa Dijon da kwallaye 8-0.

'Yan wasa Neymar Jr da takwaransa Edinson Cavani yayin da suke murnar lallasa kungiyar Dijon.
'Yan wasa Neymar Jr da takwaransa Edinson Cavani yayin da suke murnar lallasa kungiyar Dijon. sport24
Talla

Yayin wasan ne shi ma dan wasan gaba na kungiyar ta PSG Edinson Cavani, ya zura kwallo ta 156 da ya ci wa PSG, wadda ta bashi damar cinma tarihin da tsohon dan wasan kungiyar Zalatan Ibrahimovic ya kafa na zama wanda ya fi kowane ci mata kwallaye a tarihi.

Sauran ‘yan wasan da suka ci wa kungiyar ta PSG kwallaye sune, Angel Di Maria mai kwallaye 2, da kuma Kylian Mbappe da ya zura kwallo guda.

Har yanzu kungiyar PSG ba ta yi rashin nasara a gida ba cikin kakar wasa ta bana, kuma a halin yanzu tana matsayi na daya a teburin gasar Ligue 1 ta Faransa, inda ta bai wa kungiyar Lyon da ke biye da ita a matsayi na biyu maki 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.