Isa ga babban shafi
Wasanni

Babu sunan Neymar da Kane cikin tawagar 'yan wasan UEFA

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta bayyana sunayen gwarzayen ‘yan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, a matsayin ‘yan wasan gaba, na tawagar da ta zaba cikin shekarar 2017, wadda ta saba yin haka a kowace shekara.

Lionel Messi na kungiyar Barcelona yayinda suke gaisawa da Cristiano Ronaldo na kungiyar Real Madrid.
Lionel Messi na kungiyar Barcelona yayinda suke gaisawa da Cristiano Ronaldo na kungiyar Real Madrid. Reuters
Talla

A duk shekara hukumar UEFA ke zabar kwararrun ‘yan wasan da suka nuna bajinta a kungiyoyi da kuma kasashensu wajen fitar da tagawar.

Sauran ‘yan wasan da ke tawagar ta UEFA sun hada da, Eden Hazard na Chelsea, Kevin de Bruyne na Manchester City, Toni Kroos da kuma Luka Modric dukkaninsu da ke kungiyar Real Madrid.

‘Yan wasan baya da UEFA ta zaba kuwa sune Sergio Ramos, Marcelo, dukkaninsu ‘yan Real Madrid da kuma dani Alves na kungiyar PSG.

Mai tsaron gida kuwa da ya ciri tutar zama gawarzon UEFA na shekarar 2017, shi ne Gianluigi Buffon na kungiyar Juventus.

Wasu daga cikin ‘yan wasan da basu samu shiga wannan tawaga ta UEFA ba, kuma ake ganin suna matukar nuna kwazo da kwarewa sun hada da, Harry Kane na Tottenham, Neymar da ke kungiyar PSG, N’golo Kante na Chelsea, sai kuma David de Gea mai tsaron gida na Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.