Isa ga babban shafi
wasanni

Juventus na fatan rama abin da Real Madrid ta yi ma ta

Yau za a fafata tsakanin Juventus da Real Madrid a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a filin wasa na Allianz, in da Juventus ke fatan rama abin da Madrid ta yi ma ta a bara.

Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe da suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai a bara
Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe da suka yi a gasar cin kofin zakarun Turai a bara rfi
Talla

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane na bukatar kare kanbin da kungiyar ke rike da shi a karo na uku a jere.

Sai dai Juventus za ta yi kokarin rama abin da Real Madrid ta yi ma ta a bara, in da ta casa ta a wasan karshe na wannan gasa da ci 4-1 a birnin Cardiff.

Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya bukaci ‘yan wasansa da su maimata rawar da suka taka a minti na 45 na farko a karawar da suka yi da Madrid a bara, in da suka barke kwallon da Madrid ta fara zura mu su.

A bangare guda ana saran gwarzon dan kwallon duniya, Christiano Ronaldo zai buga wasan na yau bayan an hutar da shi a wasan da Real Madrid ta doke Las Palmas da ci 3-0 a gasar La Liga a ranar Aasabar.

Kazalika Sergio Ramos da Isco duk sun yi atisaye don kintsawa wasan na yau.

Ita ma dai Sevilla za ta yi kokarin kafa tarihi ta hanyar doke Bayern Munich da ta lashe kofin zakarun Turai sau biyar.

Matukar dai Sevilla ta samu nasara akan Bayern Munich, to zai kasance a karon farko kenan da ta tsallaka matakin wasan dab da na karshe a gasar ta zakarun Turai kamar yadda Kocinta Vincenzo Montella ya bayyana.

Kocin ya ce, za su yi wasan na yau ne da dukkanin abin da suke da shi.

Akwai yiwuwar dai, Sevilla ta tabuka abin kirki lura da cewa, ita ce ta fitar da Manchester United daga wannan gasa da jumullar kwallaye 2-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.