Isa ga babban shafi
Wasanni

Tottenham ta samu nasarar farko cikin shekaru 28 kan Chelsea

A karon farko cikin shekaru 28, kungiar kwallon kafa ta Tottenham ta casa Chelsea da kwallaye  3-1 a fafatawar da suka yi a jiya Lahadi a gasar firimiya ta Ingila.

Dan wasan Tottenham, Delle Alli na murnar samun nasara akan Chelsea
Dan wasan Tottenham, Delle Alli na murnar samun nasara akan Chelsea REUTERS
Talla

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya jinjina wa dan wasansa, Dele Alli bisa namijin kokarinsa, in da ya zura kwallaye biyu shi kadai.

Chelsea ce dai ta fara zura kwallon farko a minti na 30 ta hannun Alvaro Morata, amma Christian Eriksen ya farke a minti na 45 kafin daga bisa Alli ya kara kwallaye biyu a mintina na 62 da kuma 66.

Pochettino ya kwatanta Dele Alli da mayakin da ya cire mu su kitse a wuta duk da cewa ya samu kansa a cikin wani yanayi na rashin tabuka abin kirki a wasannin da ya yi a baya-bayan nan da suka hada da wanda ya buga wa kasarsa ta Ingila a wasan sada zumunta da Netherlands duk da cewa mintina 22 ya yi a fili.

Sannan kuma an ajiye shi a banci a wasan da Ingilar ta yi kunnen doki 1-1 da Italiya.

Chelsea dai ta lashe wasanni uku ne kacal daga cikin wasanni tara da ta buga a cikin wannan shekara ta 2018 a gasar firimiya gabanin Tottenham ta doke ta a gidanta a jiya Lahadi.

Ita ma dai Arsenal ta samu nasara akan Stoke City da kwallaye 3-0 a karawar da suka yi jiya.

Arsenal ta zura dukkanin kwallayen ne ana saura minti 15 a tashi wasan.

Da farko ‘yan kallon da suka halarci wasan a Emirates sun yi wa tawagar Arsenal ihu musamman ganin yadda Aaron Ramsey ya gaza zura kwallo a minti na 45 duk da cewa ya samu kyakkyawar dama.

Pierre-Emerik Aubameyang ne ya zura kwallaye biyu, yayin da Alexandre Lacazette ya zura ta uku.

Duk da wannan nasara dai, Arsenal ta gaza shiga jerin kungiyoyi hudu da ke saman teburi a gasar firimiya ta Ingila, abin da ke nuna cewa har yanzu tana da kalubale a gabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.