Isa ga babban shafi
Wasanni

Yawan shekaru bazai hanamu bajinta a wasanni ba - Rossi

Shahararren dan tseren gudun babur Valentino Rossi dan Italia mai shekaru 39, ya yi alla wadai da masu sukarsa, da kuma mai tsaron gida na tawagar kwallon kafar Italiya Gianluigi Buffon, saboda kin ritaya daga wasanni da suka yi duk da yawan shekarunsu.

Gwarzon dan wasan tseren babur na duniya Valentino Rossi a hannun hagu, da kuma mai tsaron gida na tawagar kwallon kafar kasar Italiya Gianluigi Buffon.
Gwarzon dan wasan tseren babur na duniya Valentino Rossi a hannun hagu, da kuma mai tsaron gida na tawagar kwallon kafar kasar Italiya Gianluigi Buffon. AFP/Twitter
Talla

Rossi wanda ya taba lashe kofin gasar Tseren babur ta duniya, ya mayarwa da masu sukarsu raddi ne bayan da ya rattaba hannu akan sabuwar yarjejeniya ta shekaru 2 da kamfanin Yamaha, da yake wakilta a gasar tseren Babur, wanda zata kare a tsakiyar shekrar 2020.

Rossi ya shawarci Buffon wanda a yanzu yake da shekaru 40 ya kwaikwaye shi wajen ci gaba da fafatawa a fagen wasanni har sai inda karfinsu ya kare.

Tun a shekarar 1996 Rossi ya fara tseren babur, kuma a cewarsa har yanzu jin sa yake garau sumul da karsashi tamkar yanzu ya fara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.