Isa ga babban shafi
Wasanni

Buffon zai koma bugawa kasarsa wasanni

Shahararren mai tsaron gida da ke kungiyar Juventus, Gianlugi Buffon, ya ce a shirye yake, ya janye ritayar da ya yi daga buga wasanni a matakin kasa, domin ya koma bugawa kasarsa ta Italiya wasa.

Mai tsaron gida na kungiyar Juventus kuma na kasar Italiya, Gianluigi Buffon.
Mai tsaron gida na kungiyar Juventus kuma na kasar Italiya, Gianluigi Buffon. Marco BERTORELLO / AFP
Talla

A baya Buffon ya sanar da yin ritaya daga bugawa Italiya wasa ne bayan da suka gaza samun tikitin halartar gasar cin kofin duniya da za’a yi a kasar Rasha.

Rashin nasarar da Italiya ta yi a hannun kasar Sweden ne, ya hana mata damar zuwa Rasha, wanda kuma karo na farko kenan da Italiya ta gaza samun nasarar halartar, gasar cin kofin duniya cikin shekaru 60.

Shi ma a nasshi bangaren, mai horar da tawagar Italiya, Luigi Di Biagio, ya ce zai sake bai wa Buffon dama a wasan sada zumuncin da zasu yi da kasashen Argentina da Ingila a ranakun 23 da kuma 27 ga watan Maris da zamu shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.