Isa ga babban shafi
Wasanni

Andrea Pirlo ya yi ritaya daga kwallon kafa

Shahararren dan kwallon kafa mai buga lambar tsakiya, Andrea Pirlo na kasar Italiya, ya sanar da yin ritaya daga wasa.

Dan wasan kasar Italiya Andrea Pirlo yayin atasaye da tawagar kasarsa a filin wasa na Pernambuco Arena da ke Recife.
Dan wasan kasar Italiya Andrea Pirlo yayin atasaye da tawagar kasarsa a filin wasa na Pernambuco Arena da ke Recife. REUTERS/Marcos Brindicci
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata ne Pirlo mai shekaru 38 ya bugawa kungiyarsa ta New York City wasa na karshe inda suka lallasa Colombus da kwallaye 2-0 a gasar kwallon kafa ta Amurka.

A baya Andrea Pirlo wanda ke lambar tsakiya, ya taba bugawa kingiyoyin AC Milan, Inter Milan sai kuma kungiyar Juventus, inda daga nan ne a karshen kakar wasa ta 2014/2015 ya koma kungiyar New York City da ke Amurka.

A shekarun da ya shafe yana buga wasa Pirlo ya taimakawa kasarsa ta Italiya cin kofin duniya na shekarar 2006, ya taimakawa AC Milan lashe kofin zakarun nahiyar turai biyu, sai kuma lashe kofunan gasar Seria A ta Italiya 2 tare da AC Milan din, yayinda ya lashe wasu kofunan gasar 4, da kungiyar Juventus.

Ya bugawa Italiya wasanni 116 ya ci kwallaye 13, a tsawon shekaru 13 da ya shafe yana bugawa kasarsa tasa wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.