"Argentina za ta doke Najeriya a Rasha"
Tsohon kocin Argentina da ya jagoranci kasar wajen lashe kofin duniya a shekarar 1978 Luis Menotti ya ce, kai tsaye tawagar kasar za ta samu maki uku a rukunin da ta fada a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a badi.
Wallafawa ranar:
Argentina na cikin rukuni guda da Najeriya, kuma a ranar 26 ga watan Junin 2018 ne kasashen biyu za su fafata a Rasha.
Tarihi ya nuna cewa, sau hudu Argentina da Najeriya suka hadu a matakin rukuni a gasar cin kofin duniya, kuma Argentiana ce ke samun nasara akan Najeriya da banbacin kwallo guda.
Tsohon kocin ya ce, ba zai yi mamaki ba idan Croatia ta casa Argentina amma a cewarsa, babu shakka kasar za ta samu maki akan Iceland da Najeriya a mataki rukuninsu na D.
A cikin watan jiya ne, Najeriya ta doke Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta amma masharhanta na cewa, wannan ba wani abu bane idan aka kwatanta da fafatawar da za su yi a gasar cin kofin duniya a Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu