Isa ga babban shafi
Wasanni

Rooney ya zazzagawa West Ham kwallaye 3 a raga

Dan wasan Everton, Wayne Rooney, ya nuna bacinta jiya laraba a filin wasa inda ya zazzagawa West Ham kwallaye 3 a raga, a wasan da kungiyar ta yi nasara ci 4-0 a gasar frimiya ta Ingila.

Wayne Rooney
Wayne Rooney Reuters/Carl Recine
Talla

Kwallayen da Rooney ya zura ya taimakawa Kungiyar haye matsayi na 13 daga na 17 a teburi.

Rooney ya ce wannan wasa shine mafi kyau da ya taba zurawa, kuma ya ji dadin kasancewa karo na farko kenan da ya ke ci wa Everton kwallaye 3 a wasa guda.

Rooney ya zura kwallaye ne mintina 18 da 28 da 66, kafin daga bisani Willaims ya zura tasa ana da minti 78.

An dai buga wasan ne kan idon Sam Allardyce da ke shirin karban jagoranci Everton a matsayin sabon koci.

Ita ma Arsenal ta lalasa Huddersfield ci 5-0.

Kocin kungiyar Arsene Wenger ya yabawa Mesut Ozil da ya taimaka wajen tabbatar da cewa sun yi wa Huddersfield kane-kane.

Ozil ya zura kwallo guda da bada taimako wajen zura 2, wanda yanzu haka ya bai wa kungiyar daman samun nasara a wasanni 7 na Frimiya da ta ke bugawa a gida.

Wenger ya ce a koda yaushe Ozil na sake bayyana sabbin kwarewarsa da Salo

A sauran wasanni frimiyar kuma

Burnley 2-1 Bournemouth

Chelsea ta sha kyar a hannu Swansea ci 1-0, a wasan da Kocinta Antonio Conte ya nemi gafarar alkalin wasa Neil Swarbrick sakamakon korasa daga filin wasa da aka yi lokacin da ya kalubalanci aikin alkalin.

Conte dai ya karasa kallon wasan ne daga dakin shiryawan ‘yan wasa.

Man City 2-1 Southampton

Liverpool 3-0 Stoke city

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.