Najeriya za ta kara da Argentina a gasar cin kofin duniya
An kammala fitar da jadawalin kasashen da za su fafata a gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa a Rasha, in da Najeriya ta fada rukuni guda da Argentina.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Najeriya dai ta samu nasarar doke Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta da suka yi gabanin fitar da wannan jadawalin.
Gabanin fitar da jadawalin na kasashe 32, mai horar da tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr ya ce, ba shi da fargaba kan kasashen da Najeriya za ta kara da su a Rasha.
Rohr ya ce, babu wata kasa mai rauni daga cikin kasashen 32 a wannan gasa ta cin kofin duniya kuma kowa na da burin taka gagarumar rawa.
Ga cikakken jadawalin kasashen da rukunin da suka fada:
RUKUNIN A
Rasha
Saudi Arabia
Masar
Uruguay
RUKUNIN B
Portugal
Spain
Morocco
Iran
RUKUNIN C
Faransa
Australia
Peru
Denmark
RUKUNIN D
Argentina
Iceland
Croatia
Nigeria
RUKUNIN E
Brazil
Switzerland
Costa Rica
Serbia
RUKUNIN F
Germany
Mexico
Sweden
South Korea
RUKUNIN G
Belgium
Panama
Tunisia
England
RUKUNIN H
Poland
Senegal
Colombia
Japan
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu