Isa ga babban shafi
Wasanni

Pep Guardiola ya bukaci FIFA ta kara yawan canjin 'yan wasa

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, ya bukaci FIFA ta karawa kungiyoyin kwallon kafa damar yin canjin ‘yan wasa daga uku zuwa biyar ko shida.

Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola
Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola
Talla

Guardiola mai shekaru 45 ya ce matakin zai taimakawa ‘yan wasa damar samun isasshen hutu yayin fafata wasa.

Ya kuma ce hakan zai rage yawan ‘yan wasan da ke samun raunuka tsakanin kungiyoyi, duba da cewa masu kwallon kafa basu faye samun isasshen hutu ba, tsakanin wasannin da suke bugawa, a kungiyoyinsu ko matakin kasashe.

A cikin watan Janairu na sabuwar shekara, hukumar FIFA zata cinmma matsayar tabbatar da karin yawan kasashen da zasu rika halartar gasar cin kofin Duniya ko kuma akasin haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.