Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta gargadi Ingila da Scotland

Hukumar FIFA ta gargadi Ingila da Scotland akan za su iya fuskantar hukunci mai tsauri idan har ‘yan wasansu suka sabawa al’adar daura bakin kyalle a hannu domin nuna alhini.

Wales ma ta bukaci FIFa ta amince 'yan wasanta su daura alamar alhini a wasansu da Serbia
Wales ma ta bukaci FIFa ta amince 'yan wasanta su daura alamar alhini a wasansu da Serbia Reuters / Carl Recine Livepic
Talla

Hukumomin kwallon kafa na kasashen Ingila da Scotland sun sha alwashin saba ka’idar ta FIFA da ta haramta sanya tufafin da ke nuna alama ko nasaba da siyasa ko addini ko kasuwanci a lokacin wasa.

Kasashen na shirin daura bakin kyalle mai dauke da tambari ja a fafatawar da za su yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a filin wasa na Wembley na neman shiga gasar cin kofin duniya.

Ranar ta zo daidai da ranar da aka amince da yarjejeniyar kawo karshen yakin duniya na 1 a 1918.

Sakatariyar FIFA Fatima Samba Samoura ta ce ya dace kasashen su bi tsarin FIFA kamar sauran mambobinta 211.

Al’adar FIFA dai ana daura bakin kyalle a hannu domin nuna alhinin mutuwa ko wata annoba ko bala’in kamar girgizan kasa.

A yau Alhamis ake sa ran shugabannin kwallon kafa na Ingila da Scotland za su gana da jami’an FIFA kan batun a Wembley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.