Isa ga babban shafi
FIFA

An nada Samaoura matsayin Sakatariyar FIFA

‘Yar kasar Senegal Fatma Samoura aka nada matsayin sakatariyar hukumaar FIFA a yau Juma’a wacce ta kasance mace ta farko da ta rike babban mukamin.

'Yar Senegal Fatma Samoura
'Yar Senegal Fatma Samoura STEPHANE DE SAKUTIN / AFP
Talla

An nada Samoura ne a babban taron FIFA da ake gudanarwa a Mexico

Samoura dai na aiki ne a Najeriya a matsayin jekadiya ga ayyukan ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya. Kuma ta shafe shekaru sama da 20 tana aiki a Majalisar Dinkin Duniya

Sakatare Janar na FIFA dai shi ne na biyu bayan mukamin shugaban hukumar.

Tuni dai kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya jiyo majiyoyi a taron na Mexico na tabbatar da mace za a nada matsayin mukamin sakatare Janar na FIFA kuma wacce ba baturiya ba.

Badakalar rashawa ce dai ta yi awon gaba da Jerome Valcke na Faransa wanda aka haramtawa harakar kwallo na tsawon shekaru 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.