‘Yan Sanda sun binciki ofishin UEFA
Bayan bayanan sirrin da aka bankado na Panama kan sabon shugaban FIFA Gianni Infantino, a jiya ‘yan sandan kasar Switzerland sun kai farmaki ofishin hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA a birnin Nyon domin bincike kan bayanan wata kwangilar da Infantino ya sanya wa hannu.
Wallafawa ranar:
Takardun Panama sun kwarmata cewa Infantino ya sanya wa wasu kamfanonin Argentina biyu hannu kan samun ‘yancin haska wasannin gasar zakarun Turai da wasu wasannin a talebijin.
Kuma tuni Juan Pedro Damiani na kwamitin da’a na FIFA kuma daya daga cikin wadanda aka ambata a bayanan sirrin na Panama ya bayyana yin murabus, domin shi ne wakilin kwangilar tsakanin UEFA da attajirin Argentina Hugo Jinkis da dan shi Mariano.
Amma Infantino ya fito ya karyata zargin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu