Isa ga babban shafi
FIFA

Tsohon shugaban FIFA Havelange ya rasu

Tsohon shugaban FIFA Joao Havelange ya rasu wanda ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24 tsakanin 1974 zuwa 1998. Ya rasu ne a cibiyar shi birnin Rio na Brazil yana da shekaru 100 a duniya.

Joao Havelange ya rasu ne a wata asibiti a birnin  Rio de Janeiro.
Joao Havelange ya rasu ne a wata asibiti a birnin Rio de Janeiro. REUTERS/Bruno Domingos
Talla

Sepp Blatter ne ya gaje shi wanda ya kasance shugaban FIFA na farko da ya fito daga wata nahiya sabanin Nahiyar Turai.

Ya taka rawa sosai wajen inganta harakar kwallon kafa a duniya, kamar yadda Shugaban FIFA na yanzu Gianni Infantino ya ce Havelange ya cancanci yabo a duniyar tamola.

Havelange dan wasan iyon ruwa ne wanda ya taba wakiltar Brazil a wasannin Olympics da aka gudanar a Berlin a shekarar 1936.

Ya taba zama cikin kwamitin shirya wasannin Olympic.

Yanzu haka kuma sunan shi aka saka a filin wasan Olympics a Rio daya daga cikin wuraren da ake wasannin a Rio a bana.

Shugaban kwamitin Olympics Thomas Bach ya ce za a sassauta tuta a filayen wasannin na Rio saboda rasuwar Havelange.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.