Isa ga babban shafi
FIFA

Gwarzon Duniya: FIFA ta bude kofa ga kowa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bullo da wani sabon tsarin da zai ba masoya kwallon kafa damar zaben gwarzon dan wasan duniya a bana.

Shugaban FIFA Gianni Infantino
Shugaban FIFA Gianni Infantino REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

FIFA ta bullo da sabon tsarin ne bayan kawancenta da mujallar Faransa da ke bayar da kayautar Balon d’Or ya kawo karshe.

A ranar 9 ga watan Janairu ne FIFA za ta bayar da kyautar a Zurich

A sabon tsarin na FIFA, an ware kashi 50 ga koca kocai na kasashen duniya da kuma kaftin kaftin yayin da sakamakon sauran kashi 50 zai fito daga kuri’un ‘yan jaridu da kuma masoya kwallon kafa a fadin duniya da za su jefa kuri’a ta intanet.

Kafin karshen mako nan ake sa ran FIFA za ta sanar da ‘yan wasa 23 da za a zabi 3 daga cikinsu a watan Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.