Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Suarez ya karbi takalmin zinari

Luis Suarez ya lashe kyautar takalmin Zinari bayan ya kasance wanda ya fi yawan jefa kwallaye a raga a wasannin lig lig a Nahiyar Turai. Dan wasan ya lashe kyautar ne da yawan kwallaye 59 da ya jefa a raga a kakar wasan da ta gabata.

Luis Suarez ya lashe takalmin Zinari a Turai
Luis Suarez ya lashe takalmin Zinari a Turai REUTERS
Talla

A La liga kwallaye 40 Suarez ya jefa wa Barcelona a raga a wasanni 35.

Bayan karbar kyautar Suarez ya godewa abokan wasan a Barcelona da ya ce sun taimaka ma shi cimma burin shi.

Shekarar da Luis suarez ya zo Barcelona ya taimaka wa kungiyar lashe kofuna uku da suka hada da La liga da Copa del Ray da kofin Zakarun Turai, sannan a kakar da ta gabata ya lashe wa kungiyar kofuna biyu.

Wannan ne karo na biyu da Suarez ya lashe kyautar bayan ya taba karbar takalmin zinarin a lokacin da yana Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.