Isa ga babban shafi
Wasanni

Blatter zai yi hannun riga da kujerarsa

Da yiwuwar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter ya yi hannun riga da kujersa a karshen wannan makon sakamakon bakadalar cin hanci da rashawa da hukumar ta FIFA ke fama da ita.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Sepp Blatter
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Sepp Blatter REUTERS/Arnd Wiegmann/Files
Talla

Dama dai Blatter mai shekrau 79 da haihuwa ya shirya ajiye mukaminsa a cikin watan Fabairu shekarar badi, to sai dai kuma hukumomin kasar Switzwerland sun kaddamar da bincike a kansa a yanzu dangane da zargin da ake masa na cin hanci da rashwa, lamarin da ake ganin zai sa ya bar kujerersa nan bada jimawa ba.

Blatter dai ya musanta aikata wani laifi, amma  ana zarginsa da biyan dalar Amurka miliyan 2 ba bisa ka'ida ba ga Michel Platini a watan Fabairun shekarar 2011, inda ya ce ya biya Platini kudaden ne sakamakon wani aiki da ya yi wa FIFA tsakanin shekarar 1999 zuwa shekarar 2002..

A cewar Masharta  abin tambaya anan shine mai yasa bai biya kudaden ba nan take har sai bayan kusan shekaru 10 da yin aikin?

Shima dai Platini, wanda shine shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai,  ana zargin sa da hannu a wannan badalakkalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.