Isa ga babban shafi
Wasanni

Afrika ta kudu za ta binciki Jami'an hukumar kwallon kasar

Jami’an Yan Sandan Afrika ta kudu za su gudanar da bincike na musamman kan wasu manyan jami’an hukumar kwallon kafar kasar biyu game da zargin cin hanci da rashawa a lokacin da Kasar ta ta dau bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudu Danny Jordaan.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudu Danny Jordaan. AFP PHOTO / GORDON HARNOLS
Talla

Ana zargin Shugaban hukumar kwallon kafar kasar na yanzu Danny Jordaan da tsohon shugaban hukumar Molefi Oliphant da hannu a cin hancin.

Afrika ta kudu ta bada dalar Amurka miliyan 10 wanda ta ce ta bayar ne domin bunkasa harkar kwallon kafa tsakaniun 'Yan Afrika dake zaune a kasashen yankin Carribean.

To sai dai Amurka ta musanta haka tare da fadin cewa kudaden wadanda aka sanya a wani asusu dake karkakshin ikon Jack Warner, tsohon mataimakin shugaban FIFA, an bada su ne a matsayin cin hanci domin baiwa kasar izinin daukan bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.