Kosovo za ta zama mamba a UEFA
Kasar Kosovo zata gabatar da wata takardar neman izinin zama mamba a hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA.
Wallafawa ranar:
Kosovo za ta gabatar da takardar ne a taron da hukmar ta UEFA za ta gudanar a cikin watan mayun shekarar badi a babban birnin
Buadapest na Kasar Hunagary.
Matukar idan ta zama Mamba a hukumar, to hakan zai baiwa tawagarta da sauran kungiyoyin kwallon kafar Kasar damar buga gasa dabam dabam da hukumar ke shirya wa a Turai.
A wani taro na kwanaki biyu da aka gudanar a kasar Malta, kwamitin zartarwa na UEFA ya bayyana cewa Kosovo na da cikken damar da za ta nemi kujera a hukumar.
Kawo yanzu dai kasashe 54 mambobi a hukumar kwallon kafar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu