Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho ya mayar wa Gerrad martani kan Terry

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya mayar da martini ga Steven Gerrad, game da batun ajiye dan wasan sa John Terrry a banci a wasan da Chelsa ta lallasa Maccabi Tel Aviv da ci 4-0 a jiya laraba a gasar Cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho
Kocin Chelsea, Jose Mourinho Reuters
Talla

Steven Gerrad wanda a ya koma da taka leda a LA Galaxy ya kalli wasan na Chelsea da Maccabi Tel Aviv ta kafar talabijin tare da yin nazari kan yadda wasan ya gudana yayin da kuma ya bayyana cewa Mourinho ya ajiye Terry a banci ne saboda sabanin dake tsakaninsu.

Kana ya ce ya kamata Terry ya buga wasan tunda shine kyaftain din Chelsea wato jagoran yan wasan kungiyar.

To sai dai a cewar Mourinho, Gerrad ya yi kuskure a zancen sa kuma ya musanta cewa akwai rashin jituwa a tsakainsa da dan wasan.

Mourinho dai ya yanke shawarar ajiye Terry ne a banci tun lokacin da Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester City.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.