Isa ga babban shafi
Wasanni

David De Gea ya samu Matsalar kulla kwantiragi da Real Madrid

Da alama dai Komawar David De Gea mai tsaron gidan Manchester United zuwa Real Madrid ya rushe saboda rashin kammala takardun yarjejeniyar kan lokaci.Lamarin da ke zuwa yayin da ya rage sauran sa'o'i kalilan a rufe fagen Siyan 'yan wasannin a kaka bana.

Wikimedia/Ivan
Talla

Duk da dai har yanzu kungiyoyin biyu ba su ce komai ba kan wannan batun ba, a ba ya dai Manchester united ta amince za ta siyarwa Madrid ne dan wasan kan fam miliyan 29.

Tsaikon da aka samu kuma ya biyo bayan dagewar da United ta yi cewa sai dai su yi musayar 'yan wasa, a inda ta bukaci bayar da De Gea sannan Real Madrid ta ba ta Sergio Ramos.

Yayin da shi kuma mai tsaron bayan Real Madrid Ramos ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a kungiyar.

Shi kuwa Adnan Januzaj ya koma Borussia Dortmund, sai mai tsraon gida Anders Lindegaard na shi kuma ya kulla kwatiragi da west brom

A na ta bangare kuma Chelsea na fatan kammala kulla yarjejeniyar  da dan wasan kasar Senegal Papy Dji-lobodji wanda ke bugawa Nantes na Faransa kan Fam miliyan 4.

Kocin Chelsea Jose Mourinho a yanzu dai ya karkata ne wajen kammala wannan yarjejeniya bayan rashin samun nasara kulla kwantiragi da John stones na Everton
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.