Isa ga babban shafi
Wasanni

Pellegrini ya tsawaita zamansa a Manchester City

Manajan Manchester United Manuel Pellegrini ya tsawaita kwantiraginsa da Manchester city kuma yanzu haka zai ci gaba da jan ragamar Kungiyar har nanda da shekara ta 2017. 

Manajan Manchester City Manuel Pellegrini
Manajan Manchester City Manuel Pellegrini Photo: Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Kocin ya bayyana cewa sabon kwantiragin da ya kulla da Kungiyar, alama ce da ke nuna irin kwarin gwiwar da Club din ke da shi a kansa.

Pellegrini mai shekaru 61 kuma dan asalin kasar Chile ya kara da cewa, yana da matukar muhimmaci a gareshi ya kai Klub din ga gaci.

A watan yunin shekara ta 2013 ne ya karbi aikin horar da kungiyar ta Manchester City, inda ya maye gurbin Roberto Mancini.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.