CAF ta yi watsi da bukatar Musa Bility na takarar FIFA
Hukumar kwallon kafar nahiyar Africa CAF ta ki amince ta goyawa Musa Bility na liberia baya, domin tsayawa takarar maye gurbin Sepp Blatter shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya wato FIFA
Wallafawa ranar:
Bayan gudanar da wani tattaunawa da suka yi shugabannin hukumar ta CAF sun nuna cewa, ba za su marawa Musa Bilitiny baya ba kamar yadda ya bukata, daga wajen hukumar sai dai tana masa fatan alheri a harkokin sa na kasuwanci.
Tun dai a cikin watan Yuni da ya gabata ne Bility wanda shine shugaban hukumar kwallon kafa Liberia tun shekarar 2010 kawo yanzu, ya nuna sha’awarsa na tsayawa wannan takara.
Yanzu dai haka Zico fitaccen dan wasan Brazil da ya yi tashe a baya da kuma attajirin kasar Korea ta kudu Chung Mong-Joon sune suka nuna sha'awarsu na karawa a neman wannan kujera.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu