CAF
CAF ta dakatar da Morocco daga shiga gasar cin kofin Afrika
Hukumar CAF da ke kula da kwallon Kafa a Afrika ta dakatar da kasar Morocco daga shiga gasar cin kofin Afrika da za a gudanar a 2017 da 2019 bayan kasar ta ki karbar bakuncin gasar da ake gudanarwa a kasar Equatorial Guinea saboda tsoron cutar Ebola.
Wallafawa ranar:
Talla
CAF kuma ta ci tarar Morocco kudi dalar Amurka miliyan guda.
CAF ta dauki wannan matakin ne a kan Morocco bayan an kai zagayen karshe a gasar cin kofin Afrika da Equatorial Guinea ta karbi bakunci.
A ranar Lahadi kasar Cote’Ivoire za ta fafata da Ghana a wasan karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu