Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Ouattara ya dankara wa ‘Yan wasan Cote d’Ivoire kudi

Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya ba ‘Yan wasan kasar ladar kudade da suka kai euro Miliyan 3 sakamakon nasarar da suka samu na lashe kofin Afrika. A kasar Equatorial Guinea. Cote d’Ivoire ta lashe kofin ne bayan ta doke Ghana a wasan karshe.

Alassane Ouattara tare da Yaya Touré da dubban mutanen kasar Cote d'Ivoire a Abidjan
Alassane Ouattara tare da Yaya Touré da dubban mutanen kasar Cote d'Ivoire a Abidjan REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Gwamnatin Cote d’Ivoire ta ba kocin kasar Herve Renard kudi da suka kai euro 114,000. Sannan an ba dukkanin ‘yan wasan kasar gida da darajarsa ta kai euro 46,000 hadi da ladar kudi.

Gwamnatin Ouattara ta ba hukumar kwallon kafa a kasar kyautar kudi da suka kai euro 380,000

Baya ga kyautar kudi da gida, gwamnatin ta karrama ‘yan wasan kasar da kyautar lambar yabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.