Isa ga babban shafi
CAN 2015

Cote d’Ivoire ta lashe kofin Afrika

Kasar Cote d’Ivoire ta lashe kofin gasar Afrika bayan ta samu sa’ar kasar Ghana a bugun fanariti da suka fafata a wasan karshe a kasar Equatorial Guinea. Kocin ‘yan wasan Cote d’Ivoire Herve Renard ya sadaukar da nasarar lashe kofin ga al’ummar Cote d’Ivoire.

'Yan wasan Cote d'Ivoire suna murnar lashe kofin Afrika a kasar Equatorial Guinea
'Yan wasan Cote d'Ivoire suna murnar lashe kofin Afrika a kasar Equatorial Guinea REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Wannan ne dai karo na biyu da Cote d’Ivoire ke lashe kofin Afrika tun shekarar 1992 da ta lashe kofin a karon farko bayan ta doke Ghana

A jiya Lahadi Cote d’Ivoire ta samu sa’ar Ghana ne a bugun fanariti bayan sun kammala wasa babu wanda ya jefa kwallo a raga.

A lokacin da ya ke bayyana farin cikinsa Kocin ‘yan wasan kasar Cote d’Ivoire Herve Renard ya ce sun sadaukar da wannan nasarar ga al’umma Cote d’ivoire.

Renard ya shiga sahun koca-kocan Afrika da suka lashe kofin Afrika sama da daya bayan ya lashe wa Zambia kofin gasar a 2012. Kuma yanzu shi ne koci na farko da ya lashe kofin a kasashe biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.