Isa ga babban shafi
CAN 2015

CAF ta ci Eq Guinea tarar kudi

Hukumar kwallon Afrika ta ci tarar Equatorial Guinea kudi dala dubu dari saboda rikicin da magoya bayan kasar suka haddsa a filin wasa bayan sun sha kashi a hannun Ghana. ‘Yan kallo kusan 36 aka tabbatar da cewa sun jikkata a rikicin day a faru a Malabo a ranar Alhamis.

Hargitsi a wasa tsakanin Ghana da Guinée équatoriale a gasar cin kofin Afrika
Hargitsi a wasa tsakanin Ghana da Guinée équatoriale a gasar cin kofin Afrika REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Duk da rikicin daga magoya bayan Equatorial Guinea da ke karbar bakuncin gasar, hukumar CAF ta amince ‘yan kallo su shiga wasan neman na uku da kasar za ta kara da Jamhuriyar Congo a gobe Assabar.

Ghana dai ta doke Equatorial Guinea ci 3 da 0, wanda ya ba ‘yan wasan Black Stars kai wa zagayen karshe inda za su hadu da ‘yan wasan Cote d’Ivoire a ranar Lahadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.