Isa ga babban shafi
Champions League

Tsokacin Koca Kocai da ‘Yan wasa bayan hada kungiyoyi a zagaye na biyu

Bayan hada kungiyoyin da za su kara da juna a gasar Zakarun Turai zagaye na Biyu, shugabannin Kungiyoyin kwallon kafa da ‘Yan wasa da masu horar da su sun yi tsokaci akan yadda suke kallon wasanin za su kasance tare da bayyana fatarsu a kafafen yada labarai.

Jose Mourinho na Real Madrid da Sir Alex Ferguson na Manchester United
Jose Mourinho na Real Madrid da Sir Alex Ferguson na Manchester United Reuters
Talla

Real Madrid da Manchester United

Sakataren kungiyar Manchester United John Alexander, yace wannan wasa ne da kowa zai so ya kalla, amma kuma karawa ce da masoya kwallon kafa za su so ace sai a zagayen karshe kungiyoyin za su hadu.

Mista John yace yana fatar Allah ya dora su akan Mourinho kamar yadda suka samu nasarar Madrid a wasan karshe da aka gudanar a 1968 a filin wasa na Wembley.

A daya bangaren kuma Direktan Real Madrid, Emilio kuma tsohon dan wasan kungiyar, yace wannan babbar wasa ce ga Ronaldo wanda zai kai ziyara Old Traffod, tare da fatar zai taimakawa Real Madrid tsallakewa zagaye na gaba.

Galatasaray da Schalke 04

Kocin Schalke, Jens Keller yace duk da cewa babu karamar kungiya a gasar Zakarun Turai amma ya ga alamun za su iya tsallakewa zagaye na gaba.

A wasa tsakanin Celtic da Juventus, Kocin Celtic Neil Lennon yace samun nasarar doke Juventus babban abu ne amma kuma samun tsallakewa sai sun yi da gaske.

A nasar bangaren kuma Direktan Juventus Pavel Nedved yace Celtic ita ce kungiya a bana da ta samu nasarar doke Barcelona don haka wannan sako ne ga Juventus.

Arsenal da Bayern Munich

Dan wasan Arsenal Lukas Podolski yace suna iya doke Bayenr Munich duk da sun buga wasan karshe da Chelsea a bara.

Amma kuma shugaban Bayern Munich Karl-Heinz a nasa bayanin yace sun san Arsenal Sosai kuma sun ji dadi da aka hada su amma kuma hakan ba zai zama hanyar da za su yi kwance ba domin sai sun yi kokarin zira kwallo a raga a Emirate.

Shakhtar Donetsk da Borussia Dortmund

Shugaban Dortmund yace be so aka hada su da Shakhtar Donetsk ba domin ana iya mutuwar kasko a wasan sai dai kuma yace kokarin da suka nuna a zagayen farko ya nuna suna iya fuskantar duk wata kungiya.

AC Milan da Barcelona

Shugaban AC Milan Silvio Berlusconi yace wasa da Barcelona ya yi dai dai. Amma yace hakan ya fara wuce gona da iri domin har yanzu suna neman hanyoyin da za su karya lagon Barcelona bayan haduwarsu sau huhu a bara. Berlusconi yace a shekarun baya Barccelona da Madrid ba tsararsu ba ne don haka suna neman hanyoyin farfado da wannan martabar.

A na sa bangaren kuma Jagoran Barcelona Carles Puyol ya yada a Twiter cewa yaji dadi da aka hada su da Milan ba wai don suna da taushi ba illa yana son wasa da AC Milan.

Rahotanni dai sun ce kocin Barcelona Tito Vilanova ya fara farfadowa bayan an yi masa tiyata a jiya Alhamis wanda zai sa kocin ya kwashe tsawon Makwanni shida yana jinya. Kuma ana sa ran zai dawo Gab da wasa tsakanin Barcelona da AC Milan a gasar Zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.