An hada Milan da Barcelona, Madrid da United
A Gasar zakarun Turai kungiyar AC Milan za ta hadu da Barcelona yayin da kuma aka hada Real Madrid da Manchester United a zagaye na biyu. Kungiyar Arsenal ce kuma za ta fara karbar bakuncin Bayern Munich inda kuma aka hada Shakhtar Donetsk da Borussia Dortmund.
Wallafawa ranar:
Barcelona da ta lashe kofin a shekarar 2009 da 2011 yanzu haka tazarar maki 9 ne taba Atletico Madrid a Teburin La liga. Kuma Yanzu an hada ta wasa ne da AC Milan kamar yadda kungiyoyin biyu suka hadu a bara.
A daya bangaren kuma an hada Manchester United da Real Madrid inda Cristiano Ronaldo zai kai ziyara Old Trafford.
A shekarar 2003 Manchester da Real Madrid sun taba haduwa inda Ronaldo na Brazil ya taimakawa Real Madrid doke United da jimillar kwallaye ci 6-5 a zagayen Kwata Final.
Sauran kungiyoyin da aka hada akwai:
Galatasaray da Schalke 04
Celtic da Juventus
Arsenal da Bayern Munich
Shakhtar Donetsk da Borussia Dortmund (GER)
Valencia da Paris Saint-Germain
FC Porto da Malaga
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu