Isa ga babban shafi
Spain

Clasico: Barcelona 3 Real Madrid 2

Kungiyar Barcelona ta doke Real Madrid ci 3-2 a wasan neman lashe Super Cup karawar farko da kungiyoyin biyu suka fafata a filin wasa na Nou Camp, kafin su sake haduwa a Bernabeu.

Dan wasan Barcelona Xavi yana murnar zira kwallo a ragar Real Madrid kusa da Sami Khedira  a wasan neman lashe Super Cup a Nou Camp
Dan wasan Barcelona Xavi yana murnar zira kwallo a ragar Real Madrid kusa da Sami Khedira a wasan neman lashe Super Cup a Nou Camp REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Cristiano Ronaldo ne ya fara zirawa Madrid kwallo a ragar Barcelona bayan dawowa hutun rabin lokaci, amma nan take ne Barcelona ta barke kwallon a kafar Pedro.

Lionel Messi da Xavi Hernandez sune suka zirawa Barcelona sauran kwallayen biyu. Amma kuma Angel Di Maria shi ne ya kada kwallo a ragar Barcelona bayan kwace kwallon a kafar Victor Daldes.

Mourinho yace yana ganin pedro ya jefa kwallon farko ne yana barawon gida. Amma dai ya amsa Barcelona sun buga masa kwallo. Kamar yadda Vilanova yace ya gamsu da yadda ‘yan wasan shi suka taka leda a haduwar shi ta farko da Mourinho.

A Bernebeu ne za’a yi karawar karshe, kuma anan ne za’a fitar da gwani tsakanin kungiyoyin biyu a bana.

Tuni Jose Mourinho kocin Real Madrid yace yafi bukatar ya lashe kofin La liga a bana, da ya lashe Super Cup. Kodayake yace duk da kofin baya da wani tasiri a kakar wasa amma yana son ya lashe kofin idan har zai karawa ‘Yan wasan shi kwarin gwiwar sake lashe kofin La liga a bana.

A Spain dai ana buga Super Cup ne tsakanin kungiyar da ta lashe kofin La liga da kuma kungiyar da ta lashe Kings Cup ko kuma Copa del Rey.

Wannan ne haduwar Mourinho da Vilanova ta farko a Clasico, kodayake Vilanova shi ne mataimakin Guardiola wadanda suka haramtawa Mourinho kofin La liga sau uku a jere.

Mourinho yace babu wani sauyi da aka samu a Barcelona domin ‘Yan wasan ne da ya sani bayan tambayarsa ko yana ganin za’a samu sauyi a zamanin Vilanova wanda ya gaji Guardiola.

A bara dai Barcelona ce ta lashe Super Cup bayan doke Real Madrid ci 3-2 a Bernabeu, a lokacin ne kuma Mourinho ya tsokane Vilanova a ido.

A ranar Lahadi kungiyoyin biyu suka fara buga La liga, kuma Bercelona ta lallasa Real Sociedad ci 5-1, amma Real Madrid ta yi kunnen doki ne ci 1-1 da Velencia.

Amma kafin su sake haduwa a karshen mako ranar lahadi Real Madrid za ta bakunci getafe a La liga, Barcelona ma ta kai ziyara Osasuna. Valencia kuma ta karbi bakunci Deportivo La Coruna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.