Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Alex Song yace ya yi farin cikin komawa Barcelona

Alex Song na Kamaru yace gurin shi ya cika bayan ya koma taka kwallo a Barcelona daga Arsenal wanda aka yi cinikinsa akan kudi Euro Miliyan 19. Alex Song yace yana farin komawa Barcelona, domin ita ce kungiyar da babu irinta a Duniya.

Hoton Alexandre Song kusa da Tambarin kungiyar  FC Barcelona.
Hoton Alexandre Song kusa da Tambarin kungiyar FC Barcelona. PHOTO: ÀLEX CAPARRÓS-FCB.
Talla

A cewar Song ‘yayansa biyu masoyan Messi ne, kullun sukan yi maganar shi, amma kuma yanzu zasu kara yin farin ciki domin ya zama abokin wasan Messi.

Kocin Arsenal Arsen Wenger yace Arsenal zata haska a bana duk da ficewar Zaratan ‘Yan wasanta, hakan kuma ya biyo bayan ficewar Alex Song da Robin Van Persie.

A karawar Farko a Premier, wasa tsakanin Arsenal da Sunderland an tashi ne babu ci, kuma ficewar Van Persie da Song ya nuna a bana Arsenal sai ta yi da gaske kafin kawo karshen yunwar Kofin da take yi tsawon shekaru 7.

Kodayake Arsene Wenger yace zai yi kokarin Cefanen ‘yan wasa kafin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasan a ranar 31 ga wannan watan na Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.